Bayyana yin bismilla a ya yin sallah.
Tambaya
Mene ne hukuncin bayyana bismilla a ya yin sallah bayyananniya?
Amsa
Dangane da bayyana bismillah a sallah wani abu ne ya ke cikin abubuwa na sabanin malamai, wasu malaman fikihun su na ganin wajabcin bayyana bismilla a sallah, ya yin da wasu daga cikinsu ke ganin boye karanta bismillah shine mafi dacewa, wannan al’amarin abun kididdigewa ne a cikar sallah, don haka babu mamaki a samu sabani a cikinsa, lamarinsa abu ne mai yalwa.
Abin da ya kamata limamai su lura da shi anan shine, abin da aka saba gudanarwa a masallatai da garuruwa – Na bayyanawa ko boyewa – to shi ya kamata suyi, hakan zai nesanta samar da sabani da rarrabuwar kai, tare da shagaltar da mutane da abu na furu’a fiye da na asali.
Arabic
Englsh
French
Deutsch
Urdu
Pashto
Swahili
